Home Labaru Siyasar Zamfara: Yariman Bakura Ya Sha Alwashin Ba Matawalle Goyon Baya

Siyasar Zamfara: Yariman Bakura Ya Sha Alwashin Ba Matawalle Goyon Baya

1127
0

Shugaban jam’iyyar APC na Zamfara Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura, ya dauki alkawarin mara wa gwamnatin jam’iyyar PDP a jihar baya.

Sanata Ahmed Sani, ya bada tabbacin ne a lokacin da ya kai ziyarar ban-girma ga gwamnan jihar Dakta Bello Matawalle a gidan gwamnati da ke Gusau.

Ya ce babu shakka, kasancewar Natawalle a matsayin gwamnan jihar Zamfara nufi ne na Allah, kuma duk wanda ya yi yunkurin kalubalantar wannan matsaya bai yi imani da Allah ba.

Sanatan ya kara da cewam ya je ne domin ya taya Matawalle murna, tare da ba shi tabbacin goyon bayan domin ci-gaban jihar.

Ya kuma bada tabbacin cewa, duk magoya bayan shi za su mara wa Matawalle baya, kuma za su cigaba da jan hankulan mutane domin bada cikakken goyon bayan su, musamman da shawarwarin da za su kawo ci-gaban jihar.


Leave a Reply