Home Ilimi Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-Rufa’i

Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-Rufa’i

57
0

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU reshen jihar Kaduna, ta ki komawa bakin aiki duk da barazanar da gwamna Nasir El-Rufai ya yi na korar su.

Hukumar kula da jami’ar KASU dai ta bukaci daliban da su koma karatu domin yin jarrabawar su bayan barazanar da gwamnan ya yi.

A ranar Litinin din da ta gabata, an ga wasu daga cikin daliban KASU su na rubuta jarabawar su a karkashin kulawar mataimakin shugaban jami’ar da sauran ma’aikatan cibiyar.

Wata majiya ta ce, ‘yan kungiyar ASUU reshen Jami’ar KASU sun ki shiga aikin kula da daliban masu rubuta jarrabawa, inda su ka yi ikirarin cewa har yanzu su na cikin yajin aiki.