Home Labarai Solomon Dalung Ya Bayanna Dalilin Da Ya Sa Ake Ficewa Daga APC

Solomon Dalung Ya Bayanna Dalilin Da Ya Sa Ake Ficewa Daga APC

31
0

Jam’iyyar APC na kara fuskantar barazanar sauyin sheka yayin da zaben shekara ta 2023 ke karatowa.

Tsohon ministan matasa da harkokin wasanni Solomon Dalung, ya ce jam’iyyar APC ta bijire wa manufofin farko da su ka kai ga kafa ta.

Ya ce Jam’iyyar APC ta dauki tafarkin jam’iyyar PDP, wadda tsarin ta bai dace da tsarin dimokradiyya ba, da kuma tilasta wa ‘yan Nijeriya a kan wasu ‘yan takara, lamarin da ya ce shi ya sa ya yi ban-kwana da ita.

Masana kimiyyar siyasa a Nijeriya dai na alakanta dabi’ar sauya sheka a siyasance da rashin akida ko manufa a siyasa, da uwa-uba son kai kamar yadda Dakta Faruk BB Faruk ya bayyana.

Tuni dai shugaban jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana bakin ciki game da neman shawo kan ‘yan jam’iyyar musaman daga majalisar dattawa da adadin masu ficewa zuwa wasu jam’iyyu ke kara yawa.