Home Labaru An Yi Jana’Izar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara Da Ya Rasu A Hannun...

An Yi Jana’Izar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara Da Ya Rasu A Hannun ‘Yan Bindiga

6
0
Muazu-Magarya Zamfara Speaker

An gudanar da sallar jana’izar mahaifin kakakin majalisar dokoki ta jihar Zamfara Mu’azu Magarya.

Sheikh Ahmed Umar Kanoma ne ya jagoranci sallar jana’izar a gidan kakakin majalisar da ke Gada-biyu a birnin Gusau, duk kuwa da cewa ba a gano gawar mamacin ba.

Da ya ke yi wa manema labarai karin haske jim kadan bayan sallar jana’izar, Kwamishinan Harkokin Addini na jihar Zamfara Sheikh Tukur Sani Jangebe, ya ce za a iya yin sallar jana’izar musulmin da ya mutu yayin da gawar sa ke wani wuri.

Ya ce ana yin sallar jana’izar da ake kira ‘Salatul Gha’ib’ ga Musulmin da ya mutu kuma ba a ga gawar sa ba.

Maharan dai sun saki ‘yan kakakin majalisar guda biyar, amma sun sanar da cewa mahaifin kakakin majalisar ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a maboyar su.