Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya ce
dattawan kudancin Kaduna sun gurza wa mataimakan sa ‘dan
asalin yankin rashin mutuncin da ba ya misaltuwa.
El-Rufa’i, ya kuma bayyana dalilan da su ka sa ya zaɓi mace musulma ‘yar asalin yankin kudancin Kaduna a matsayin mataimakiyar sa.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen bikin kaddamar da littafi da ritayar Ishaq Akintola, wanda ya kafa kungiyar kare hakkin musulmi ta Nijeriya MURIC a Legas.
Ya ce a shekara ta A 2015 da ya zaɓi Barnabas Bantex a matsayin mataimakin sa, dattawan Kudancin Kaduna sun nuna bacin ran su matuka, inda su ka rika sukar sa suna yi ma shi habaici da cewa shi mayaudari ne kuma ba ya da amana, kawai don bai dauki zaɓin kungiyar Kiristoci ba.
Har Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya kammala mulkin sa a jihar Kaduna dai, babu ga maciji tsakanin sa da dattawa da mutanen yankin Kudancin jihar Kaduna.