Home Labaru Rashawa Ta Yi Katutu Zamanin Buhari – Bishop Kukah

Rashawa Ta Yi Katutu Zamanin Buhari – Bishop Kukah

260
0

Shugaban ɗariƙar Katolika a yankin Sokoto Bishop Mathew
Hassan Kukah, ya ce ba a taɓa cin rashawa a Nijeriya ba
kamar zamanin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Bishop Kukah ya bayyana haka ne, yayin da ke jawabi a wajen bikin cikar Babalola shekaru 60 da zama lauya, inda ya ce duk da dai ba a mulkin Buhari aka fara cin rashawa a Nijeriya ba, amma lamarin yafi muni a zamanin sa.

Ya ce a gwamanatin Muhammadu Buhari sun ga mafi nunin cin hanci da rashawa ta fannin tarbiyya da hada-hadar kuɗi da ma fannoni da dama.

Bishop Mathew Kukah, ya kuma koka da yadda shugabanni ke tattare ayyukan ci-gaban al’umma zuwa yankunan da su ka fito, ya na mai cewa hakan ba zai taimaka wajen bunƙasa dimokraɗiyya a Nijeriya ba.

Leave a Reply