Home Home Yadda CBN Ya Ba Gwamnatin Buhari Bashin Naira Tiriliyan 23.8 Ba Bisa...

Yadda CBN Ya Ba Gwamnatin Buhari Bashin Naira Tiriliyan 23.8 Ba Bisa Ƙa’ida Ba

396
0
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta kawo cikas ga kokarin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ke yi na kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele bisa zargin daukar nauyin ta’addanci.

Alamu na nuni da cewa zaune ta tashi tsaye a Majalisar Dattawa, yayin da su ka gano cewa Babban Bankin Nijeriya ya ba Gwamnatin tarayya rancen tsabar kuɗi har naira tiriliyan 23 da biliyan 800 a cikin shekaru bakwai ba bisa ƙa’ida ba.

A ranar Larabar da ta gabata ne, shugaba Buhari ya yi ƙoƙarin neman amincewar Majalisar Dattawa, ta sa hannun cewa ta amince bankin CBN ta bada bashin, wanda an riga an karɓa kuma an kashe kudaden.

Dokar CBN dai ta ce, idan gwamnatin tarayya ta na fama da giɓin kasafin kuɗaɗe, za ta iya rancen kuɗi daga bankin CBN, amma adadin da bankin zai bada kada ya wuce kashi 5 cikin 100 na jimlar kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar da ta gabata. Bashin da gwamnatin tarayya ta ci daga bankin CBN ba bisa ƙa’ida ba dai ya karya doka, kuma ya haifar da tsadar rayuwa da ƙuncin rayuwa da hauhawar farashi da gurguncewar tattalin arziki da kuma jibga ɗimbin bashi a wuyan kowane ɗan Nijeriya, har m da waɗanda za a haifa nan da shekaru masu zuwa.

LEAVE A REPLY