Home Labaru Yadda Aka Yi Wa Talakawa Wala-Walar Ayyuka 73 A Ondo Da Gundumar...

Yadda Aka Yi Wa Talakawa Wala-Walar Ayyuka 73 A Ondo Da Gundumar Abuja

12
0

Wata ƙungiya mai bin-diddigin yadda ake gudanar da ayyukan mazaɓu daga kasafin gwamnatin tarayya, ta fallasa wani binciken da ta yi tsakanin jihar Ondo da Gundumar Ƙananan Hukumomin birnin tarayya Abuja.

Kungiyar dai, ta bi diddigin ayyukan da aka ware kuɗaɗe aka ce an yi a cikin kasafin shekara ta 2019 da 2020.

Ta ce an ware naira biliyan 3 da miliyan 905 domin gudanar da ayyukan raya mazaɓu a yankuna 86 na shiyyar Ɗan Majalisar Tarayya 9 cikin yankin Sanatoci uku na jihar Ondo, amma ayyuka 30 kaɗai ƙungiyar ta iya ganowa.

Kungiyar ta kara da cewa, daga cikin ayyukan 30 ɗin ma akwai waɗanda an watsar da su ba a kammala ba, sauran 56 kuma an rasa inda su ke ko inda aka yi da su.

Ta ce a yankin birnin Abuja an ware Naira biliyan 1 da miliyan 245 domin a yi ayyuka 17, sai dai Daraktan ƙungiyar Dakta Daisi Omokingbe, ya ce aiki ɗaya kacal su ka iya ganowa an kammala, sauran 16 babu wanda ya san inda aka yi su ko kuma yadda aka yi da maƙudan kuɗaɗen da aka ware domin a yi wa talakawa ayyukan.