Iyayen yara a jihar Zamfara, sun yi kira ga gwamnati ta dubi yiwuwar bude makarantu domin hana dalibai ci-gaba da gararamba a kan tituna.
Makarantun firamare da na sakandare a jihar Zamfara dai sun kasance a rufe tsawon watanni biyu, a wani bangare na tsaurara matakan tsaro sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Tun a ranar 1 ga watan Satumba na shekara ta 2021 ne, gwamna Matawalle ya sanar da rufe makarantun firamare da sakandare a fadin jihar Zamfara, biyo bayan zafafa kai hare-hare a makarantun.
Tuni dai wasu iyayen sun fara nuna fargaba a kan yadda babu wani bayani da ke fitowa daga bakin hukumomin jihar game da batun bude makarantun, duk kuwa da samun haske a yakin da ake yi da ‘yan bindigar.














































