Yayin taron malajisar zartarwa ta kasa na makon da ya gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya sake jefa zukatan Ministocin sa cikin dar-dar game da makomar su a wa’adin mulkin shi na biyu.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, ana sa ran wasu daga cikin Ministocin za su cigaba da rike mukaman su, ganin cewa shugaba Buhari ba ya da niyyar sauya masu aiki tare da shi.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata, shugaba Buhari ya kara wa gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele wa’adin shekaru 5, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan Nijeriya game da wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka.
Wasu na ganin cewa Godwin Emefiele ya na da kafa a fadar shugaban kasa, saboda kusancin da ya ke da shi da wasu na-hannun-daman shugaba Buhari.
Rahoton ya nuna cewa, ko da wasu Ministocin ba su tabuka wani abin a zo a gani ba, za a iya kafa sabuwar gwamnati da su muddin su na da masu tsaya masu a fadar shugaban kasa.
You must log in to post a comment.