Home Labaru Rashin Tsaro: Shugaba Buhari Zai Sabonta Alkawarin Da Ya Dauka Na Kawo...

Rashin Tsaro: Shugaba Buhari Zai Sabonta Alkawarin Da Ya Dauka Na Kawo Karshen Kashe-Kashe-Wamakko

217
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu  Buhari ya sabonta alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta magance lamarin rashin tsaro a Najeriya.

Dan majalisar  dattawa mai wakiltan yankin Sokoto ta arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayyana hakan ne a madadin shugaban kasa a lokacin da ya kai ziyara ga wadanda harin yan bindiga ya rutsa da su a karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto.

Shugaban kasa Muhammadu  Buhari

Wamakko ya mika kayayyakin tallafi ga shugaban jam’iyyar All APC a karamar hukumar Goronyo, Kabitu Sarki Fulanin Goronyo,  domin a rarrabawa mutanen da abin ya shafa.

Hare-haren ya janyo mutuwar mutane 29, a yayin da wasu kuma suka bar gidanjensu a yankin.