Dan Majalisar dattawa mai wakiltar Jhar Zamfara ta yamma,
Abdul’aziz Abubakar Yari na shirin raba tirela 358 na kayan
abinci iri-iri daban-daban.
Kayayyakin da za a raba sun hada da; shinkafa da gero da suga da masara.
Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Kungiyar Siyasa ta A Yari, Ibrahim Muhammed, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Gusau.
Ya ce za a raba kayan abincin ne don taimakawa mutane wajen gudanar da azumin watan Ramadana ga kowa da kowa ba tare Bda la’akari da bambancin siyasa ba.
A cewarsa, an shirya tsarin rabon a karkashin kungiyar siyasa ta A Yari bisa jagorancin Lawal Limana wanda ake sa ran magidanta dubu17,500 za su ci gajiyar rabon.
Muhammad ya bayar da tabbacin cewa kananan hukumomi 13 cikin 14 na jihar za su ci gajiyar shirin.
Ya bayyana cewa sama da kashi 98 cikin 100 na kayayyakin tuni an yi nasarar jigilarsu zuwa kananan hukumomi daban- daban na jihar, wanda hakan ya sa wadanda za su ci gajiyar tallafin za su samu nasu kason kan lokaci.














































