Home Labaru Makomar Kane, Ronaldo, Mbappe, Coutinho, Locatelli Da Rudiger

Makomar Kane, Ronaldo, Mbappe, Coutinho, Locatelli Da Rudiger

96
0
Makomar Kane, Ronaldo, Mbappe, Coutinho, Locatelli Da Rudiger

Manchester City ta shirya sayen ɗan wasan gaban Ingila Harry Kane daga Tottenham a kan fam miliyan 127.

Kane mai shekaru 28 na fatan sanin makomarsa a Tottenham daga nan zuwa mako mai zuwa, bayan sun buga wasansu na farko a gasar Premier League din ta bana da Manchester City da ke son sayensa. (Telegraph, subscription required)

Ita kuwa jaridar (AS – in Spanish ta ce Paris St-German na duba yiwuwar sayan ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo daga Juventus, a kasuwar cinikin yan wasa ta 2022.

PSG na fatan Ronaldo, mai shekaru 36, ya maye gurbin Kylian Mbappe da Real Madrid ke nema.

Ana rade-radin tsohon ɗan wasan Liverpool Philippe Coutinho da yanzu ke wasa a Barcelona zai dawo tsohuwar ƙungiyar tasa. (Liverpool Echo)

Haka kuma Liverpool na da sha’awar ɗauko Jeremy Doku daga Rennes na Faransa, da ake sa ran su nemi wajen fam miliyan 38 ga ɗan wasan mai shekaru 19, in ji (Voetbal24 – in Dutch).