
‘Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 25 da su ka haɗa da Hakimi da wasu sarakunan gargajiya a ƙaramar hukumar Bukkuyyum ta jihar Zamfara.
Maharan, sun afka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadin da ta gabata su ka kashe mutanen, kamar yadda mazauna yankin su ka shaida wa manema labarai.
Mutanen garin sun ce, ‘yan bindigar sun shiga garin Ganar Kiyawa ne a kan babura, bayan mutane sun tsorata su ka rika harbin su.
Daga cikin waɗanda aka kashe kuwa har da hakimin garin Bala Muhammadu da Magajin gari Sani Salihu da wani bafade da ake kira Sharu.
Wani mazaunin garin ya ce da shi da Hakimi da Magajin Garin sun yi gudun tsawon kilomita uku, yayin da su ka cimma su ne su ka tambayi Magajin Gari me ya ke yi wa gudu ya ce wahala, nan take su k ace to ta ƙare su ka bude ma shi wuta.













































