Home Home Nema Mafita: Buhari Ya Kira Ministan Lantarki Kan Matsalar Wuta Da Ake...

Nema Mafita: Buhari Ya Kira Ministan Lantarki Kan Matsalar Wuta Da Ake Fama Da Ita

40
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kira Ministan Lantarki Abubakar Aliyu domin ganawa a sirrance a fadar shi da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kira Ministan Lantarki Abubakar Aliyu domin ganawa a sirrance a fadar shi da ke Abuja.

Ana sa ran shugaba Buhari zai tattauna da Ministan ne kan matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a fadin Nijeriya.

Wannan, ya na dauke ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasaGarba Shehu ya fitar. Shugaba Buhari, ya kuma kira Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da mai ba shi shawara a kan tattalin arziki Doyin Salami domin ganawa da su.