Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai rushe dukkan masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin sa ranar 22 ga watan Mayu, bayan ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya a ranar, kamar yadda ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ya bayyana.
Lai Mohammed ya sanar da haka, yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta kasa a Abuja.
Idan dai za a iya tunawa, mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari zai tafi hutu zuwa kasar Ingila bayan kammala ziyarar aiki a jihar Borno.
Ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai dawo Nijeriya a ranar 5 ga watan Mayu, kwanaki 17 zuwa ranar da zai rushe dukkan mukaman siyasar da ya nada.
You must log in to post a comment.