Home Labaru Wata Sabuwa: Sau 50 Mayakan Boko Haram Na Neman Hallaka Ni –...

Wata Sabuwa: Sau 50 Mayakan Boko Haram Na Neman Hallaka Ni – Zulum

38
0
Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Kawo ‘Yan Sintiri 150 Daga Kasar Kamaru
Boko Haram - Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ce akalla ya tsallake rijiya da baya sau sama da 50 sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai ma shi don neman hallaka shi.

Yayin ganawa da manema labarai bayan ya ziyarci shugaban Muhammadu Buhari a Abuja, Zulum ya ce rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar al’ummar jihar Borno sama da dubu 100, yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Zulum ya kara da cewa, ya zuwa yanzu mayakan Boko Haram dubu 2 da 600 su ka tuba, ciki kuwa har da mata da kananan yara.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin sa ba ta tunanin ba tubabbun mayakan ko sisin kwabo don su ajiye makaman su, yayin da ya ce ya gana da shugaban kasa a kan makomar su da kuma bayyana dalilin da zai sa a karbe su a cikin al’umma.