Home Home Wata Sabuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi A Saka Dokar Ta-Ɓaci Kan Kisan...

Wata Sabuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi A Saka Dokar Ta-Ɓaci Kan Kisan Gilla Don Yin Tsafi

145
0

Majalisar Wakilai ta nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana dokar ta-ɓaci kan aikata kashe-kashe don yin tsafi a faɗin ƙasar.

Kiran na cikin ƙudirorin da wakilan suka cimma a zamansu na yau Laraba bayan gabatar da wani ƙudirin gaggawa kan rayuwar jama’a mai taken ‘Need to Curb the Rising Trend of Ritual Killings in Nigeria’ wato – buƙatar daƙile kisan gilla don aikata tsafi a Najeriya.

Shugaban Marasa Rinjaye Toby Okechukwu ne ya gabatar da ƙudirin.

Buƙatar tasu na zuwa ne yayin da ake samun rahotannin kisan gilla da zimmar neman kuɗi ta hanyar tsafi a sassan Najeriya, wanda na baya-bayan nan shi ne Sofiat Okeowo a Jihar Ogun.

‘Yan majalisar sun yi kira ga hukumar wayar da kai ta ƙasa National Orientation Agency (NOA) da iyaye da shugabannin makarantu da malaman addini da ‘yan jarida da su fara kamfe don daƙile ci gaba da faruwar kashe-kashen.