Home Labaru Kiwon Lafiya Wata Sabuwa: Jihar Kwara Ta Sanya Dokar Hana Fita Don Yaƙi Da...

Wata Sabuwa: Jihar Kwara Ta Sanya Dokar Hana Fita Don Yaƙi Da Cutar Korona

336
0

Gwamnatin Jihar Kwara, ta sanya dokar kulle daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 4:00 na yamma, da zummar daƙile yaɗuwar annobar cutar korona.

Umarnin kafa dokar dai ya na cikin sabbin matakan kariya daga cutar, wanda kwamitin yaƙi da korona na jihar ya fitar.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Ilorin, Kwamishinan Lafiya kuma Shugaban Kwamitin Dakta Raji Rasaq, ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 24 ga watan  Disamba na shekara ta 2020.

Sauran matakan kuma sun haɗa da dakatar da ma’aikatan gwamnati zuwa ofis, inda ma’aikatan da ya zama dole ne kaɗai za su riƙa zuwa aiki.

Kwamishinan ya ya kara da cewa, makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe har sai an ji daga gare su, kuma wajibi ne wuraren ibada kar su ɗauki mutane sama da kashi 50 cikin 100 na abin da su ka saba ɗauka domin bada tazara.