Home Labarai Wata Sabuwa: Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin...

Wata Sabuwa: Ana Son A Naɗa Betta Edu Sabon Muƙami A Gwamnatin Tinubu

46
0

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu faɗa a ji a ƙasar nan na neman dawo da dakatacciyyar Ministar Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Fatara, Betta Edu kan madafan iko.

Hakan dai na zuwa watanni biyu bayan dakatar da Betta Edu daga muƙaminta.

Kawo yanzu dai hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC da kuma fadar shugaban kasa sun bar ‘yan Najeriya cikin duhu kan mataki na gaba.

Bincike  ya nuna cewa, bayan dakatar da Edu da binciken da hukumar ta EFCC ta yi a ranar 8 ga watan Janairu, hukumar ta gudanar da cikakken bincike, kuma tuni ta miƙa rahoton wucin gadi ga fadar shugaban kasa.

An samu labarin cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta miƙa rahoton wucin gadi na binciken da ta yi kan zargin da ake yi wa ministar da aka dakatar, inda ta ba da shawarar a gurfanar da Edu a gaban kuliya.

Sai dai kuma idan aka yi la’akari da irin rawar Betta Edu ta taka wajen samun nasarar jam’iyyar APC mai mulki, akwai zargin cewa wasu masu faɗa a ji ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na matsin lamba ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ya yi duk mai yiwuwa wurin ganin ba a hukunta ta ba.

Leave a Reply