Home Labarai Shugabanci: Tinubu Ya Taka Rawar Gani Sosai-Buhari

Shugabanci: Tinubu Ya Taka Rawar Gani Sosai-Buhari

101
0

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ce magajinsa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na taka rawar gani sosai tun bayan hawansa mulki watanni tara da suka wuce.

Tsohon shugaban kasa, ya ce Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, amma ya ce Najeriya kasa ce mai wuyar sha’ani.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da wasu jami’an hukumar a Daura.

Tinubu dai ya fuskanci suka kan wasu daga cikin manufofin da ya bijiro da su game da tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur.

Wadannan tsare-tsare da sauransu sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki, tabarbarewar tattalin arziki, da faduwar darajar Naira, wanda hatta a ‘yan kwanakin nansai da aka yi zanga-zanga a fadin kasar nan.

Buhari ya ce yana da matukar wahala ga ‘yan najeriya su iya jure matsin tattalin arziki da ake fama da shi, sai dai ya ce yana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren gwamnati mai ci.

Leave a Reply