Home Labaru Wasu Maniyyatan Jihar Jigawa Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Sa’a Biyar...

Wasu Maniyyatan Jihar Jigawa Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Sa’a Biyar A Sama

110
0

Wani jirgin kamfanin Max Air dauke da maniyyata da ya tashi
daga filin jirgin sama na birnin Dutse a jihar Jigawa, ya yi
saukar gaugawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano
bayan tafiyar akalla sa’o’i biyar a sama.

Wani daga cikin maniyyatan da ke cikin jirgin ya shaida wa manema labarai cewa, su na cikin tafiya ne a cikin jirgin da ya dauko su tun da farko su ka shiga gargada, daga nan aka sanar da su cewa za su koma saboda wata mata domin a sauya masu jirgi.

Ya ce bayan sun sauka a Kano cikin ikon Allah kafin sa’a daya aka sanya su a cikin jirgin da aka sauya, bayan kwashe tsawon sa’o’I biyar a sama aka sanar da cewa za su sake komawa Kano.

Mutumin ya ce daga baya su ke jin cewa jirgin na biyu ya dawo ne saboda wata matsalar diflomasiyya, amma bayanai na nuna cewa yanzu haka maniyyatan su na dab da sake tashi a wani jirgin na daban.

Leave a Reply