Home Home Wani Sabon Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 38 A Jihar Nasarawa

Wani Sabon Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 38 A Jihar Nasarawa

136
0

Akalla mutane 38 aka tabbatar da mutuwar su ciki har da mata da kananan yara, yayin wani harin ‘yan bindiga a garin Takalafiya da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

‘Yan bindiga dai na ci-gaba da kai hare-haren Sari-Ka-Noke a kan daidaikun mutane tun bayan wata takaddama da aka samu tsakanin Makiyaya da Manoma.

Rahotanni sun ce, tun farko wani manomi ne a yankin Gwanja da ke makwabtaka da Takalafiya ya kalubalanci wani makiyayi da ya saki dabbobin sa su ka yi masa barna a gona.

Yayin takaddamar ne kuma makiyayin ya rasa ran sa, lamarin da ya haddasa rikici tsakanin bangarorin biyu.

Wata majiyar ce, a asabar da ta gabata ne al’ummar yankin su ka gudanar da jana’izar mutane 38 da ‘yan bindigar su ka kashe a kauyuka biyu.

Leave a Reply