Akalla jami’an Soji uku ne su ka mutu, yayin da wasu 10 su ka samu raunuka daban-daban a wani harin kwanton-bauna da ‘yan ta’adda ta ISWAP su kai wa ayarin motocin su, lokacin da su ka fatattaki ‘yan ta’addan a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Wata majiya ta ce sojojin da harin ya rutsa da su, sun hada da na runduna ta 3 da ta 4 ta rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa MNJTF, inda aka kai masu harin ta hanyar jefa wa ayarin motocin su Bom a kan hanyar su ta zuwa sansanin ISWAP da ke Tunbum Reza.
Majiyar ta ce daya daga cikin Boma-Boman ne ya bugi wata mota mallakin sojojin Jamhuriyar Nijar da wata mota kirar Hilux.
Majiyoyin sun ce an kashe ‘yan ta’addan da dama a harin da ba su yi nasara ba, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin ‘yan ta’addan da aka kashe ba.