Home Home Wani Jigo A APC Ya Nemi Tinubu Ya Binciki Kashe-Kashen Da Aka...

Wani Jigo A APC Ya Nemi Tinubu Ya Binciki Kashe-Kashen Da Aka Yi A Mulkin Buhari

59
0

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC Alhaji Sani Al’ameen Muhammad, ya shawarci shugaba Tinubu da ya binciki kashe-kashen da aka yi a zamanin gwamnatin Buhari domin sanin adadin ‘yan Nijeriya da aka kashe tare da biyan diyyar rayukan su.

Al’ameen dai ya bada shawarar ne yayin tattaunawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce zubar da jinin ‘yan Nijeriya babban laifi ne na cin zarafin bil’adama da ya zama dole a yi bincike.

Ya ce galibin kashe-kashen rashin hankali da garkuwa da mutane da tada kayar baya da sauran matsalolin rashin tsaro da ake fama da su, wasu ‘yan tsiraru ne masu son zuciya ke jagorantar su.

Al’ameen, yayi Allah wadai da matakan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai da tsohon shugaban hafsan sojin kasa Janar Tukur Buratai su ka dauka, domin a cewar sa dukkan su sun raina matakan shari’a.

Leave a Reply