‘Yan bindiga sun sace wasu shugabannin mata na jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
An dai sace matan ne a yankin Manini da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, bayan sun halarci bikin rantsar da sabon gwamnan jihar sanata Uba Sani.
Shugaban ƙungiyar ci-gaban masarautun Birnin Gwari Ishaq Usman Kasai ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai.
Ya ce ‘yan bindigar sun tare hanyar ne su ka sace shugabannin matan biyu na jam’iyyar APC da wasu mutane da dama su ka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Ishaq Usman Kasai, ya ce har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntuɓi iyalan su ko wani daban a yankin ba.














































