Sanata Ahmed Lawan, ya gudanar da aiki na farko a matsayin shin a sabon Shugaban majalisar dattawa, inda ya rantsar da Rochas Okorocha a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Imo ta yamma.
An dai rantsar da Okorocha ne a zauren majalisar da misalin karfe 10:30 na safe, jim kadan bayan majalisar ta gabatar da addu’o’i.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne, sanatoci su ka zabi Ahmed Lawan da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin Shugaban majalisar dattawa da mataimakin sa.
You must log in to post a comment.