Home Labarai Matsalar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Ma’Aikata Karin Albashi Da Kasha 25...

Matsalar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Ma’Aikata Karin Albashi Da Kasha 25 Zuwa 35 Cikin 100

100
0
Nigerian Flag e1628181802822 1280x720
Nigerian Flag e1628181802822 1280x720

Gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikatanta ƙarin albashi da kimanin kashi
25 cikin ɗari zuwa kashi 35 cikin ɗari. Hakan na zuwa ne a daidai
lokacin bukin ranar ma’aikata ta duniya.


A cikin wata takarda daga shugaban hukumar kula da albashi ta kasa Ekpo Nta ta tabbatar da ƙarin albashin. Takardar ta nuna cewa ƙarin albashin zai fara ne daga ranar ɗaya ga watan Janairun 2024.


Kamar akasarin al’umma ƙasar nan ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun faɗa cikin mawuyacin hali sanadiyyar matsin tattalin arziƙi. Kayan
masarufi sun yi tashin gwauron zabi sannan darajar naira ta zube idan aka kwatanta da dalar Amurka duk kuwa da sabbin matakan da
gwamnatin ƙasar ke ci gaba da ɗauka. Yanzu haka akwai wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta kafa wanda k iki tare da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa domin samar da matsaya kan ƙarancin albashi ga ma’aikata a ƙasa


A baya ƙungiyoyin ƙwadago sun sha yin barazanar shiga yajin aiki da durƙusar da lamurra a ƙasar domin tursasa wa gwamnatin tarayya ɗaukan matakan bunƙasa walwalar ma’aikata.


A halin yanzu mafi ƙarncin albashin ma’aikata a hukumance shi ne naira 30,000. Kuma duk da haka akasarin gwamnatocin jihohi ba su iya biyan ma’aikatansu albashin mafi ƙaranci, inda akan samu wasu ma’aikata na bin bashin albashin watanni da dama.

Leave a Reply