Home Home Tu’ammuli Da Kwayoyi: An Kama Dilan Kwaya Zai Kai Sansanin Boko Haram

Tu’ammuli Da Kwayoyi: An Kama Dilan Kwaya Zai Kai Sansanin Boko Haram

40
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama dillalin miyagun kwayoyi a hanyarsa ta kai wa sansanin mayakan Boko Haram da ke yankin Banki a jihar Borno.

Mutumin dai, na daga cikin manyan dilolin miyagun kwayoyi 24 da hukumar ta kama a sassan Nijeriya, ciki har da wata mata mai juna biyu da kuma wasu mata hudu.

Kakakin hukumar na kasa Femi Babafemi ya ce an kama miyagun kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogram dubu 7 da 609 a hannun dillalan kwayoyi da ke jihohi takwas.

Babafemi ya cigaba da cewa, yawancin kamen an yi shi ne a jihar Nasarawa, sakamakon yadda aka kama wata babbar mota dauke da manyan jakunkuna makare da tabar wiwi da ta taso daga jihar Ondo, sannan an kama mutane uku da ke da alaka da kayan.

 A birnin Abuja kuwa, an kama wasu mutane biyu da sinki 80 na curarriyar tabar wiwi da kuma jakunkuna 169 na tabar wiwi mai nauyin Kilogram dubu 1 da 961 a cikin wata babbar mota.

Haka kuma, a jihar Borno an kama wani mutum da ke kai wa ‘yan ta’adda kwaya a yankin Banki da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, sannan aka sake kama wata mai juna biyu da wasu dilolin kwaya shida a jihar Anambra.

Leave a Reply