Home Labarai Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Janye Daga Takarar Gwamna A PDP

Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Janye Daga Takarar Gwamna A PDP

112
0

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya janye daga takarar kujerar gwamnan jihar, gabanin zaben fidda gwani a karkashin jam’iyyar PDP.

Mahdi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren sa Umar Aminu a Gusau.

Mahdi Aliyu Gusau, ya bukaci wakilai da shugabannin jam’iyyar da magoya bayan sa da su zabi Dr. Lawal Dauda a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana dalilin Mahdi Aliyu Gusau na ficewa daga takarar ba.

Leave a Reply