Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Sace Malaman Coci A Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Sace Malaman Coci A Jihar Katsina

36
0

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, wasu ‘yan bindiga sun afka wa cocin Saint Patrick Catholic Church da ke Gidan Maikambo a karamar hukumar kafur, tare da sace malaman coci biyu da wasu kananan yara biyu.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na cocin Christopher Omotosho ya raba wa manema labarai ya tabbatar da faruwar lamarin.

Wata majiya ta ce, da tsakar dare ne ‘yan bindigar su ka afka wa cocin, inda su ka yi awon-gaba da babban limamin cocin Rabaran Stephen Ojapa, da mataimakin sa Oliver Okpara da wasu yara maza biyu da ke tare da su, sai dai har yanzu ‘yan bindigar ba su kira iyalai ko cocin domin bukatar wani abu ba.

Mr Omotosho, ya yi kira ga jama’a su sanya malaman cocin a cikin addu’ar Allah ya kubutar da su.