Home Labarai Mutane Sun Mutu a Rushewar Coci a Jihar Delta a Nijeriya

Mutane Sun Mutu a Rushewar Coci a Jihar Delta a Nijeriya

83
0

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Delta, ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon rugujewar da wani coci mai bene ya yi a birnin Asaba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Bright Edafe ya
tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce an ceto
mutane 18 daga cikin ginin, yayin da wasu mutane uku su ka ji
mummunan raunuka.

Sai dai DSP Edafe ya ƙaryata labarun da su ka ce mutane 10 ne
su ka mutu, yayin da wasu ganau ke cewa har yanzu ana ci-gaba
da aikin ceto.

DSP Bright Edafe, ya ce mutanen da ke cikin cocin su na ibada
ne a lokacin da lamarin ya faru a saman benen, don haka ginin
bai faɗa a kan wasu da ke kasa ba.

Hukumar bada agajin gaugawa ta jihar Delta, ta ce ‘yan kwana-
kwana da ‘yan sanda na ci-gaba da bincike domin gano waɗanda
su ka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin.