Home Labaru Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kashe Jagoran Masu Garkuwa Da Mutane A Hanyar...

Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kashe Jagoran Masu Garkuwa Da Mutane A Hanyar Abuja-Kaduna

488
0

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ta ce ta samu nasarar bindige babban jagoran masu garkuwa da mutane, wanda ya yi garkuwa da Shugaban Hukumar Gudanarwar ta UBEC a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An dai bindige dan ta’addan ne wani ba-ta-kashi da aka yi tsakanin mahara da ‘yan sanda a dajin Rijana da ke Karamar Hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Frank Mba ya bayyana haka, inda ya bayyana sunan dan bindigar da Sumaila Sule da aka fi sani da lakabin Shaho kuma dan asalin kauyen Rijana ne.

Jami’an tsaro dai sun bayyana Sule Shaho a matsayin kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane, wanda su ka dade su na nema ruwa a jallo.Mba ya ce, Shaho ya mutu a jijjifin asubahin ranar Asabar da ta gabata, bayan ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga da ‘yan sandan ‘Operation Puff Adder’ su ka yi masa.

Leave a Reply