Home Labaru Tsaro: Sojin Najeriya Sun Halaka Kwamandojin Boko Haram A Borno

Tsaro: Sojin Najeriya Sun Halaka Kwamandojin Boko Haram A Borno

406
0

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar hallaka wasu kwamandojin mayakan Boko Haram, ya yin gumurzun da suka yi a jihar Borno.

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce, dakarun sojin sun kaiwa mayakan samame ne akan iyakar Najeriya da Kamaru, lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa dajin Sambisa.

Sanarwar ta ce sojin Najeriyar sun kuma yi nasarar kwace makamai da tarin alburusai, Mota da kuma Kekuna.

Ma’aikatar ta ce daga cikin manyan kwamandojin na Boko Haram akalla 8 da ta halaka akwai, Ba Issoufou da ake kira da Tumbun Dabino da Amir Batam da Tumbun Bororo da kuma Koukar Kowa da Tumbun Dila.

Leave a Reply