Home Labaru Mali: Tawagar ECOWAS Ta Gabatar Da Tayin Kafa Gwamnatin Hadin Gwiwa

Mali: Tawagar ECOWAS Ta Gabatar Da Tayin Kafa Gwamnatin Hadin Gwiwa

163
0

Tawagar shiga tsakanin da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta aike zuwa Mali domin sasanta rikicin siyasar kasar, ta gabatar da tayin kafa gwamnatin hadin gwiwa, tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.

Kawo yanzu babu bangaren da ya maida martani kan tayin, wanda shi ne karo na 2 da tawagar dake karkashin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke yunkarawa, tun bayan soma aikinta a makon jiya.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A karashen makon nan ne dai kawancen ‘yan adawar na Mali yayi fatali da tayin amincewa da nada sabbin alakalan kotun tsarin mulkin kasar da aka rusa, don sake nazarin sakamakon zaben ‘yan majalisar da ya zama silar zanga-zangar kin jinin gwamnati da neman tilasatawa shugaba Ibrahim Boubacar Kieta yin murabus.

A ranar Juma’a 17 ga watan Yuli ‘yan adawar suka ce babu gudu ba ja da baya kan sharadin da suka gindaya na neman murabus din shugaba Ibrahim Boubacar Kaita.