Hukumar sadarwa ta kasa NCC ta bada umurnin yin rajistar layin waya domin kiyaye ayyukan batagari a Nijeriya.
Shugaban hukumar da ke kula da sashen masu ruwa da tsaki, Sunday Dare ya sanar da hakan a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a kan hadarin yin hulda da masu zamba a kan layukan waya wanda ya gudana a Jihar Nasarawa.
Dare ya ce, manufar yin wannan rajistar shine, domin taimakawa wajen sanin masu yin amfani da layukan wayan, a kuma samu saukin tantance masu aikata laifuka ta hanyar amfani da layukan wayan.
A karshe ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen magance matsalar masu amfani da layukan wayan da ba su da rajista, wanda hakan ya sa hukumar ta umurci masu kamfanonin wayan da su kulle duk layukan da ba su da rajista, su kuma bayar da rahoto a kan haka.
Idan dai ba a manta ba, hukumar ta ci tarar kamfanin MTN wasu tarin kudade sakamakon kin bin irin wannan doka a shekara ta 2015.