Home Labaru Kididdiga: UNICEF Ta Ce ‘Yan Boko Haram Sun Sa Yara Sama Da...

Kididdiga: UNICEF Ta Ce ‘Yan Boko Haram Sun Sa Yara Sama Da 3,500 Ayyukan

344
0

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce, kimanin yara sama dubu 3 da dari 500 ne ‘yan ta’adda suka tilastawa kai harin sari-ka-noke a yankin arewa maso gabas.

UNICEF ya ci gaba da cewa, bisa tilas aka ta horar da wasu yara kanana tare da koya musu atisayin kai hare-hare tun a shekara ta 2013.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran wanda mafi akasarin su ‘yan shekaru 13 zuwa 17 ne, an horar da su ne tsakanin shekara ta 2013 zuwa ta 2017, kuma da su ake ta gumurzun yake-yake da hare-haren da ake yi a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. Asusun ya kara da cewa, a cikin shekara ta 2018 kadai an kashe kananan yara 432, an sace 180, sannan an yi wa kananan yara mata  43 fyade, duk a yakin na Arewa maso Gabas.

Leave a Reply