Home Labaru Tsaro: Dakarun Hadin Gwiwa Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 39

Tsaro: Dakarun Hadin Gwiwa Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 39

646
0

Dakarun hadin gwiwa na kasashen tafkin Chadi, sun hallaka mayakan Boko Haram 39 a wani gumurzu da suka yi a kan iyakar Najeriya da Chadi.

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, mai dauke da sa hanun Kanar Ezindu Idima, ta ce a bangaren su, sojoji 20 sun jikkata.

Fafatawar da Runduna ta biyu a bangaren Chadi da Runduna ta uku a bangaren Najeriya suka kaddamar na farautar neman yan ta’addan mai take “Operation Yancin Tafki” ya yi sanadiyyar halaka mayakan Boko Haram da dama a kauyen Cross Kauwa dake dab da tafkin Chadi.

Idima ya ce dakarun hadin gwiwar sun kuma kwato motocin yaki biyu da wasu manyan bindigogi na harbo jiragen sama da karin wasu bindigogi masu sarrafa kansu da harsasai masu yawan gaske.

Tuni dai babban Hafsan Hafsoshin Rundunar tsaro na Chadi Janaral Tahir Erda da Babban Hafsan sojin kasa na kasar suka tsallako kan iyakar Najeriya, don jinjinawa dakarun.

Janar Erda ya kuma nemi dakarun da su gaggauta kawo karshen ta’addancin na Boko Haram akan lokaci.