Home Labaru Minimum Wage: Kano, Zamfara, Kwara, Rivers, Kogi, Edo Ready To Pay N30,000

Minimum Wage: Kano, Zamfara, Kwara, Rivers, Kogi, Edo Ready To Pay N30,000

168
0

Gwamnatocin jihohin Kano, Zamfara Kwara, Rivers, Kogi da kuma Edo, sun amince da biyan sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata na Naira dubu 30.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna muhimmanci ga harkokin jin dadin ma’aikata a jihar, tare da tabbatar da cewa basa bin ta bashi.

Shima gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin dukkanin mai yiwuwa domin ganin ma’aikatan jihar na cikin walwala da jin dadi.

A nasa bangaren gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara ya ce gwamnatinsa ta shirya tsaf domin biyan sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan da aka kayyade.

Haka ma gwamnatin jihar Kogi, ta kafa kwamiti tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta samawa jihohi yanayi mai kyau ta yadda za su iya biyan sabon albashin.