Home Labaru Tsaro: An Fara Siyasantar Da Kashe-Kashen Da Ke Aukuwa A Kaduna Da...

Tsaro: An Fara Siyasantar Da Kashe-Kashen Da Ke Aukuwa A Kaduna Da Zamfara – Buhari

265
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce babu wani lamari mai muhimmanci da gwamnatin sa ke fafutukar tabbatarwa a halin yanzu face kawo karshen ta’addanci, musamman a jihohin Kaduna da Zamfara.

Buhari ya ce, a halin yanzu babu wani shugaba a fadin duniya da ke cikin kunci kamar shi, duba da yadda ta’addancin masu garkuwa da mutane da kashe-kashe ya zama ruwan dare a jihohin Kaduna da Zamfara.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan Nijeriya da dama sun gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar da ta gabata, inda su ka koka da halin ko-in-kula da gwamnatin shugaba Buhari ke nuna wa lamarin ta’addanci a jihohin biyu, sai dai shugaban ya ce siyasa ta shiga cikin lamarin matukar za a yi masa irin wannan fahimta.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaba Buhari ba zai taba kasancewa cikin farin ciki ba, matukar jinin al’ummar sa zai cigaba da kwarara ba tare da hakki ba.

Shugaba Buhari, ya ce siyasar Nijeriya ta munana, matukar ‘yan adawa za su rika jifar shi da mugun nufi na rashin damuwa yayin da ake yi wa talakawan sa kisan kiyashi.