Home Labaru Kasuwanci Korafi: An Shigo Da Buhunnan Shinkafa Sama Da Miliyan 20 A A...

Korafi: An Shigo Da Buhunnan Shinkafa Sama Da Miliyan 20 A A Cikin Watanni Uku – RIPAN

331
0

Kungiyar Masu Casar Shinkafa ta Najeriya RIPAN, ta koka da cewa a cikin watanni uku kacal da su ka gabata, an yi fasa-kwaurin shinkafa zuwa Nijeriya da yawan ta ya kai sama da buhunna miliyan 20.

Shugaban kungiyar Mohammed Maifata ya bayyana haka, yayin da ya ke yi wa manema labarai bayani game da yawaitar shigo da shinkafa daga ketare, duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta haramta shigo da ita.

Maifata ya kara da cewa, masu fasa-kwauri su na karya kanana da manyan manoman shinkafa, kuma su na janyo wa Nijeriya asarar biliyoyin kudade zuwa kasashen waje da kuma asarar kudaden shiga.

Ya ce duk da irin matakan tsaron da ake sa wa, amma kan iyakokin Nijeriya sun koma dandalin safarar shinkafa, kuma kasuwannin Nijeriya makil su ke da shinkafar da ake fasa-kwauri daga kasashen waje.

Leave a Reply