Home Labaru Tsaro: Abinda Buhari Ya Fada Wa Shugabannin Rundunonin Tsaro Na Kasa

Tsaro: Abinda Buhari Ya Fada Wa Shugabannin Rundunonin Tsaro Na Kasa

579
0
Tsaro: Abinda Buhari Ya Fada Wa Shugabannin Rundunonin Tsaro Na Kasa
Tsaro: Abinda Buhari Ya Fada Wa Shugabannin Rundunonin Tsaro Na Kasa

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da jita-jitar da wasu ‘yan Nijeriya ke yadawa a kan taron gaugawar da shugaba Buhari ya kira shugabannin rundunonin tsaro ya na da alaka da kiran da wani sanata ya yi a kan Buhari ya yi murabus saboda gazawar sa a bangaren tsaro.

Sanata Eyinnaya Abaribe dai ya yi kira ga shugaba Buhari ya yi murabus saboda ya gaza shawo kan matsalolin tsaro da su ka addabi sassan Nijeriya.

Sai dai sakamakon wani taron gaugawa da shugaba Buhari ya yi da shugabannin rundunonin tsaron a fadar sa da ke Abuja, yasa wasu ke zargin cewa taron ba zai rasa nasaba da kiran neman Buhari ya yi murabus ba.

A cikin  wata hira da ya yi da manema labarai, kakakin shugaban kasa Garba Shehu, ya ce ko kadan babu gaskiya a zargin da wasu ke yi cewa taron ya na da nasaba da kalaman Abaribe.

Ya ce an shirya taron ne kamar yadda aka saba yi daga lokaci zuwa lokaci, ko kuma duk lokacin da bukatar hakan ta taso kamar yadda aka saba.