Home Labaru Dambarwa: Kotu Ta Nemi A Tono Mamaci Daga Kabarin Sa A Kano

Dambarwa: Kotu Ta Nemi A Tono Mamaci Daga Kabarin Sa A Kano

670
0
Dambarwa: Kotu Ta Nemi A Tono Mamaci Daga Kabarin Sa A Kano
Dambarwa: Kotu Ta Nemi A Tono Mamaci Daga Kabarin Sa A Kano

Wata Kotun shari’ar Musulunci da ke Kano, ta bada umarnin tono wani mutum daga kabarin sa bayan mako daya da binne shi.

Mataimakin shugaban hukumar Hisbah ta jihar mai kula da ayyukan musamman Sheikh Muhammad Al-bakri ne ya tabbatar wa manema labarai haka.

Kotun, a  karkashin jagorancin Mai shari’a Sani Yola ce ta bada umarnin a yi wa gawar sutura, kasancewar hukumar Hisbah ta roki kotun ta ba asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano umarnin bada gawar wani mai suna Abdullahi Obinwa ga iyalan sa domin binnewa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sai dai bayan wannan umarni ne aka samu akasin musanya gawar da ta wani dan kabilar Igbo mai suna Basil Ejensi, lamarin da ya sa wasu ‘yan kabilar Igbo garzayawa kotun Ustaz Ibrahim Sarki Yola, inda su ka bayyana wa kotun cewa an yi masu musayar gawa.

Bayan kotun ta saurari jawabin su ne ta bada umarnin a hako gawar da ta bada umarnin binnewa mako guda da ya gabata.