Home Labaru Tsadar Rayuwa: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ɗebar Wa Gwamnati Wa’adin Kwana 14

Tsadar Rayuwa: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ɗebar Wa Gwamnati Wa’adin Kwana 14

34
0

Daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago a Nijeriya
TUC, ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki goma sha
hudu domin cimma matsayar da za ta rage radadin cire tallafin
mai da ‘yan Nijeriya suka shiga ko ta fuskanci zanga-zangar
ma’aikata.

Shugaban kungiyar Nuhu Toro ya shaida wa manema labarai cewa, kungiyar ba ta ji dadin tafiyar hawainiyar da ake yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin ba.

Ya ce wani bangare na fahimtar da su ka yi da gwamnati shi ne, cewa a cikin makonni 8 ya kamata a samar da ingantattun matakan tallafin da za a iya tabbatarwa kuma za a aiwatar da shi cikin lokacin da aka amince.

Nuhu Toro ya ce an kafa wasu ƙananan kwamitoci da za su yi aiki domin warware matsalolin, amma makonni hudu bayan akan ƙananan kwamitocin uku ne kawai su ka nuna cewa sun yi wani abin a zo a gani, yayin da wasu kwamitocin ba su fara aiki ba.

Kungiyar TUC dai ta bada wa’adin ranar 19 ga watan Agusta domin kammala tattaunawa ko kuma ta dauki matakin kare ma’aikata da talakawa daga halin kuncin tattalin arziki.

Leave a Reply