Home Labaru Musulmai Sun Bukaci Gwamna Adeleke Ya Amince Da Shari’ar Musulunci A Jihar...

Musulmai Sun Bukaci Gwamna Adeleke Ya Amince Da Shari’ar Musulunci A Jihar Osun

87
0

Kungiyar musulmai ta jihar Osun, ta yi kira ga gwamnan jihar
Sanata Ademola Adeleke ya amince da shari’ar musulunci a
fadin jihar.

Shugaban ƙungigar Alhaji Mustafa Olawuyi ya yi wannan kiran, lokacin bikin murnar sabuwar shekarar musulunci ta bana a birnin Osogbo.

Musulmai daga sassa daban-daban na jihar dai sun yi dafifi a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo, inda ɗalibai su ka gudanar da fareti na musamman.

Gwamna Adeleke ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka na musamman Mr BT Salam a wajen taron, wanda sarakunan gargajiya da manyan baƙi su ka halarta.

Olawuyi ya buƙaci gwamna Adeleke ya amince da Shari’ar musulunci a jihar, bisa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya tabbatar da ‘yancin yin addini ba tare da wata tsangwama ba.

Haka kuma, ya kuma buƙaci gwamnan ya ɗauki malaman Larabci da na Islamiyyah a makarantun jihar, inda ya ce adadin yawan waɗanda ake da su a makarantu sun yi kaɗan.

Leave a Reply