Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara, kwana ɗaya bayan shugaba Buhari ya ce ya na goyon bayan takarar sa, amma ba zai saki ayyukan ofis da ke gaban sa ba ya shiga kararainar taya shi yakin neman zabe jiha-jiha ba.
A ranar Larabar da ta gabata ne, Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilin da ya sa shugaba Buhari bai fara taya Bola Tinubu yakin neman zabe ba.
A cikin wata sanarwa da mai tai maka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya na nan a matsayin sa na mai goyon bayan takarar Bola Tinubu, amma ba zai bari karakainar yakin neman zabe ta ɗauke ma shi hankali daga ayyukan sa na Shugaban Ƙasa ba.
Garba Shehu dai ya fitar da sanarwar ne, domin warware damuwar da wasu ke yi, ganin cewa tun da aka fara yakin neman zabe Buhari bai je ya taya Tinubu ba, duk kuwa da cewa shi ne Babban Kwamandan Rundunar Yaƙin neman zaben Tinubu.














































