Home Labaru Ba Mu San Yawan Sabon Kuɗin Da Muka Buga Ba – CBN

Ba Mu San Yawan Sabon Kuɗin Da Muka Buga Ba – CBN

447
0
Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shirin CBN
Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shirin CBN

Mataimakiyar gwamnan Babban Bankin Nijeriya mai kula da daidaita al’amurran kuɗi A’isha Ahmad, ta ce ba ta san adadin sabbin kuɗin da bankin CBN ya fitar domin fara amfani da su a Nijeirya ba.

A’isha Ahmad ta bayyana haka ne, lokacin da ta ke amsa tambayoyi a gaban majalisar wakilai, domin yi masu ƙarin bayani a kan tsarin taƙaita cirar kuɗi da bankin ya samar.

Yayin da ta ke amsa tambayoyin, ɗaya daga cikin ‘yan majalisar Sada Soli, ya nuna damuwa dagane da ƙarancin sababin kudin da al’umma za su fara amfani da su.

A ranar Larabar da ta gabata ne, majalisar wakilai ta buƙaci mataimakin gwamnan babban bankin ya bayyana a gaban ta, biyo bayan tafiyar da gwamnan bankin Godwin Emefeli ya yi domin a duba lafiyar sa.

Leave a Reply