Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taƙaita yawan motoci da ministocin sa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati za su yi amfani da su a tawagar su zuwa guda uku kacal, inda ya ce ba za a ƙarawa kowa ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnati, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya ce wannan wani mataki ne daga cikin matakan da gwamnatin sa ke ɗauka na rage kashe kuɗaɗen gwamnati.
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya kuma ba ministocin nasa da shugabannin hukumomi da ka da su yi amfani da masu kare lafiyar su ko jami’an tsaro da suka wuce biyar.
inda kuma ya umarci mai ba shugaban shawara kan tsaron ƙasa domin tattaunawa da sojoji da ƴansanda da sauran masu ɗamara kan yadda za a rage yawan jami’an tsaron.
Da ma dai ko a watan Janairu sai da shugaban ya ce ya ɗauki matakan rage kashe kuɗaɗen inda ya rage yawan ƴan tawagar sa yayin bulaguro ƙasar waje daga 50 zuwa 20 sannan shi kuma mataimakin shugaban ƙasa aka bar masa mutum biyar.