Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Kasuwar Hannun Jari Za Ta Habbaka Bayan An Rantsar Da...

Tattalin Arziki: Kasuwar Hannun Jari Za Ta Habbaka Bayan An Rantsar Da Buhari – Kwararru

481
0

Masana harkar kasuwar zuba hannun jari, sun ce ana sa ran kasuwa ta mike bayan an sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a Ranar 29 ga Watan Mayu na shekara ta 2019.

Masanan sun ce, darajar zuba hannun jari za ta dawo da karfin ta, da zarar shugaba Buhari ya koma a kan karagar mulki karo na biyu, musamman idan aka naɗa Ministocin da ke da sha’awar harkar kasuwanci.

Sai dai masu binciken sun ce, abin da zai iya kawo wa kasuwar zuba hannun jari cikas a Nijeriya ita ce, shari’ar da ake yi tsakanin jam’iyyun APC da PDP a kan zaben shekara ta 2019.

Masanan sun ce, rashin sanin yadda shari’ar za ta kaya na iya janyo masu hannun jari su guji zuwa Nijeriya, domin kuwa babu wanda ya san halin da siyasar Nijeriya za ta kasance.Alkaluman sun nuna cewa, an samu karancin masu zuba hannun jari a Nijeriya a farkon shekara ta 2019, idan aka kamanta da abin da aka rika samu a karshen shekara ta 2018.

Leave a Reply