Gabannin zaben shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya, alamu na nuna cewa gwamnonin jam’iyyar PDP sun fi son takwaran su na jihar Ekiti Kayode Fayemi bisa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i.
Wata majiya ta ce hankalin yawancin gwamnonin PDP bai kwanta da Nasir El-Rufa’i ba, saboda yanayin da ya dauki jam’iyyar adawa da kuma ra’ayoyin sa masu tsauri a kan wasu lamurran da su ka shafi kasa, musamman ta fannin addini.
Majiyar ta cigaba da cewa, El-Rufai na iya janye takarar sa bayan tattaunawa tsakanin gwamnonin jam’iyyar APC.
Kungiyar gwamnonin Nijeriya dai ta samar da shugabanni shida a cikin shekaru 20 da su ka gabata, wadanda su ka hada da Abdullahi Adamu na Nasarawa, da Victor Attah na jihar Akwa Ibom.Sauran sun hada da Chief Lucky Igbinedion na jihar Edo, Sanata Abubakar Bukola Saraki na jihar Kwara, da Rotimi Amaechi na jihar Rivers, da kuma na yanzu daga jihar Zamfara Abdulaziz Yari.